
Kocin Ingila Gareth Southgate ya amince a rage kashi 30 cikin 100 na albashinsa saboda coronavirus. (Sky Sports)
Kin amincewar dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 20 Jadon Sancho komawa Chelsea a wannan bazarar zai iya taimaka wa dan wasan Barcelona Philippe Coutinho, mai shekara 27, wajen komawa Stamford Bridge. (Sport, in Spanish)
Arsenal na da kwarin gwiwar cewa dan wasan Bournemouth Ryan Fraser, mai shekara 26, zai sanya hannu a yarjejeniyar komawa kungiyar idan kwantaraginsa a Bournemouth ya kare a wannan bazarar. (Teamtalk)
Ana hasashen cewa dan wasan gaba na Leicester Islam Slimani, mai shekara 31, zai koma Sporting Lisbon bayan da ya gaza tabuka abin a-zo-a-gani a Leicester. (O Jogo, via Leicester Mercury)
A gefe guda, Leicester na son dauko dan wasan Fenerbahce Hasan Ali Kaldırım, mai shekara 30, ko da yake za ta fuskanci kalubale daga Galatasaray. (Hurriyet, in Turkish)
Arsenal za ta iya yunkurin sayo dan wasan Manchester United Jesse Lingard, mai shekara 27, kafin kakar wasa mai zuwa, musamman idan bata yi nasarar mayar da dan wasan da ta aro daga Real Madrid Dani Ceballos, mai shekara 23, ya zama nata ba. (The Athletic, subscription required)
Tsohon dan wasan Leeds United Noel Whelan ya bukaci kungiyar ta bayar da aron zakakurin dan wasanta Ryan Edmondson, mai shekara 18, a kakar wasa mai zuwa. (Football Insider)
Dan wasan Everton Jonjoe Kenny, mai shekara 23, yana so ya zauna a Schalke a kakar wasa mai zuwa bayan ya ji dadin zaman aro a kungiyar ta Bundesliga. (Bild, in German)
Rangers ta fitar da jerin ‘yan wasan da za su maye gurbin dan wasan gabanta Alfredo Morelos, mai shekara 23, wanda kungiyoyin Turai da dama suke zawarcinsa. (Goal, in Spanish)
Barcelona za ta yi kokarin sayo dan wasan Borussia Dortmund Raphael Guerreiro, mai shekara 26, wanda za a sayar a kan kusan euro 25m a bazara. (Sport, in Spanish)