Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugabancin jam’iyyar APC za su dinke barakar cikin gidan da ke jihar Delta

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Delta ta fara kokarin sasanta wasu jagorinta da ke rikici, Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Talata, 9 ga watan Fubrairu.

Jaridar ta ce wasu ‘yan cikin gidan APC sun shaida mata cewa za a tura manyan wakilai da za su zauna da Ovie Omo-Agege; Festus Keyamo da Great Ogboru.

Ana samun rashin jituwa tsakanin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, Ministan kwadago na kasa, Festus Keyamo SAN.

Rahoton ya ce za kuma a zauna da babban kusan jam’iyyar APC a jihar Delta, Cif Great Ogboru.

Punch ta ce wanda zai jagoranci wannan zama na sulhu shi ne tsohon ‘dan takarar gwamnan jihar Delta a karkashin jam’iyyar Olorogun O’tega Emerhor.

Olorogun O’tega Emerhor ya bayyana haka bayan shi da mai dakinsa Rita Olorogun Emerhor sun sabunta rajistarsu na jam’iyyar APC a Evwreni, garin Ughelli.

Mista Olorogun Emerhor ya ce: “Rikicin cikin gidan da ya barko wa jam’iyyar mu daf da kuma bayan zaben 2019, ya taimaka wa PDP mai mulki a Delta.”

“Daf da 2019, mun bude kofar jam’iyyarmu domin sabon-shiga su zo cikinmu. A lokacin ne wani gungu na Ovie Omo-Agege da Great Ogboru su ka shigo mana.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *