Daily Nigerian ta ruwaito cewa 35 cikin mambobin majalisar dokokin jihar Kano 40, sun rattaba hannu domin tsige Kakakin majalisa da shugaban masu rinjaye ranar Talata.
Duk da cewa Kakakin da shugaban masu rinjayen basu bayyana dalilin da ya suka yi murabus ba, an tattaro cewa sun yi murabus ne gudun kada a tsige su a zaman ranar Talata.
Wani mamban majalisan ya bayyanawa Daily Nigerian cewa su biyun gwamnan kawai suke yiwa hidima ba mambobi ba.
“Mun yi fito na fito da su ne saboda sun yi kasa a gwiwa wajen jin dadinmu wajen gwamna. A watanni goma da suka gabata mambobi basu samu kudin mazabunsu ba, da kudadenmu da dama. Har alawus na ma’aikatan majalisa ba a biya ba na tsawon shekara daya,” acewar sa