Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Yan kallo a wani bangare na Yammacin Afirka, da Yankin Larabawa, da Kudancin Asia, da Kudancin China da kuma Taiwan sun ga yadda rana ta yi husufi a wani yanayi mai ban al’ajabi.

Maɗauka hotuna sun ɗauki hotunan husufin rana – yadda wata yake ratsawa ta tsakanin Duniya da Rana, inda ake ganin haske kaɗan.

Husufin ya faru ne a ranar tsakiyar bazara – wato rana mafi tsayi a shekara ga mazauna arewacin kusurwar duniya.

Ana yin husufin rana ne sau duk shekara daya ko biyu kuma ana iya ganinsa ne kawai a wani bangare na dan yanki a bangarorin duniya. Husufin ba ya wuce daƙiƙa 90 yake kai wa ƙololuwarsa.

Mutanen da ke zaune a nisan daruruwan kilomita daga tsakiyar kusurwar ba su ga cikakken yadda rana ta yi husufi ba, ko da yake sun ga ‘yan alamu na husufin.

Masana ilimin taurari sun ce yadda husufin yake kamar sauya kallo ne daga ƙwan lantarki mai ƙarfin 500W zuwa mai ƙarfin 30W, amma da dama a najeriya mutane basu da labarin wannan husufi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *