Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na cewa an shafe daren Lahadi, wayewar garin Litinin ana musayar wuta da ‘yan bindiga a hanyar Zaria zuwa Kaduna kusa da garin Jaji.
Kwamishinan tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin a wata tattaunawa inda ya ce lamarin ya faru ne a kusa da garin Jaji.
Ya ce tun da suka samu labarin cewa ‘yan bindigar sun kai harin, nan take aka aika da jami’an tsaro domin daƙile harin.
Wani mazaunin yankin ya ce a daren, ɓarayin sun tare hanyar da ke tsakanin Dumbi-Dutse zuwa Lamban Zango, haka kuma suka tare hanya tsakanin Jaji da Kwanar Faraƙwai.
Duk da cewa babu wasu cikakkun bayanai kan wannan harin daga kwamishinan tsaron, amma wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun kashe mutum biyu da ke cikin wata babbar mota ƙirar Luxirious, haka kuma jami’an tsaron sun kashe ‘yan bindigar har mutum biyu.