Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano tana tuhumar mutumin da ya daure dan sa a gida ba tare da cikakkiyar kulawar ciyarwa da ta kiwon lafiya ba na tsawon shekaru bakwai.

Hakan na zuwa a dai-dai lokacin da rundunar ta ceto wani matashi a unguwar Sheka da aka daure tsawon shekaru.

A ranar Alhamis din data gabata ne ‘yan sanda suka ceto matashi na farko wanda mahaifin sa Malam Aminu ya daure tsawon shekaru bakwai a cikin wani daki a gidan sa dake Unguwar Farawa a gefen birnin Kano.

V.O.A ta ruwaito cewa yanzu haka dai mahaifin wannan yaro wato Malam Aminu da matarsa na shalkwatar ‘yan sanda a Kano suna fuskantar bincike, inda har ma kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya ce, sakamakon farko na binciken ya nuna tuhumar yunkurin kisan kai a kan Malam Aminu wanda dan Asalin garin Okene ne a can jihar Kogi.

Sai dai ga alama, kungiyar Human Rights Network wadda itace ta tseguntawa ‘yan sanda halin da wannan yaro ke ciki bayan da ta samu bayanan sirri, ta nuna rashin gamsuwa akan yadda ake kula da lafiyar Aminu Ahmed a Asibitin kwararru na Murtala a nan Kano.

Hakan dai na faruwa ne a dai dai lokacin da ‘yan sandan na Kano ke cewa, sun ceto matashi na biyu dake fuskantar makamancin halin da Ahmed Amin ya fuskanta kuma suna ci gaba da bincike.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *