Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Mummunan halin da alumar garin kagara suke tsinci kansu a ciki tun bayan kwashe ya’ya’yensu daga sakadaren kagara shine ke suya a zukatan iyaye da alummar garin da jihar Neja baki daya amma Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Abubakar Gumi, ya fada a ranar Asabar cewa watakila za a sako daliban makarantar Kagara da aka sace a yau Lahadi, ganin yadda tattaunawa ke gudana tsakanin gwamnati da ‘yan fashin.

Malamin, wanda ke iya shiga dazuka domin tattaunawa, nasiha da wa’azi ga manyan ‘yan bindigan da yaransu, ya shaidawa manema labarai yiyuwar sakin daliban da ma’aikatan makarantar a jiya Asabar.

An ruwaito Malamin yana bayanin cewa, a tattaunawarsa da ‘yan bindigan, basu bayyana bukatarsu ga kudin fansa ba.

Dayake karin haske cewa yayi, ‘yan bindigan na bukatar a saki wasu daga cikin mutanensu da aka kame ne, kuma a shirye suke domin tuba da jefar da makamansu matukar gwamnati zata yafe musu.

Malamin a baya ya shiga dazukan yankin Zamfara da Katsina domin tattaunawa da shugabannin ‘yan bindigan, wanda kuma ya haifar da da mai ido kasancewar samun wasu daga cikin ‘yan bindigan sun tuba sun aje makamansu.

Ya shaida wa daya daga cikin wakilan Punch cewa tattaunawar da aka yi game da sakin yaran makarantar da ma’aikatan ta yi tafiyar hawainiya ne saboda kokarin shirya kayan aikin jigilarsu, amma ana sa ran sakinsu a yau Lahadi.

Da aka tambaye shi ko tattaunawar ta shafi kudi, sai Gumi ya ce, “A’a, a’a; ba haka bane. Idan ya shafi kudi, yana nufin aikata laifi iri daya.

“Suna cewa wadannan su ne sharuddanmu kuma za mu dakatar da wannan abu. Don haka, tattaunawa tana gudana kuma ana duba bukatunsu, wadanda suke da sauki sosai.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *