Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Miliyoyin kuri’un da aka kada jiya Talata sun karu ne kan kuri’u sama da miliyan 100 da aka jefa yayin bude runfunan zabe da wuri, yayin da Amurkawa ke zabar shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin Amurka, da jami’an jihohi da na kananan hukumomi. Ana tsammanin yawan masu jefa kuri’a zai yi sama duk da rikice-rikicen da annobar coronavirus ta haifar.

A cikin sa’o’i masu zuwa, za a mai da hankali sosai ga kidayar kuri’un a jihohin Florida da North Carolina – wadanda dukkaninsu suka taimaka wajen ingiza Trump zuwa nasara a shekarar 2016, kuma inda zaben jin ra’ayin masu jefa kuri’a a wannan shekara ya nuna Trump da Biden suna kankankan da juna. Yankin gabashin jihar Pennsylvania da ake kira fagen daga, kuma shine akafi mai da hankali, amma ba lalle bane a fitar da cikakken sakamako ba har sai ya dauki tsawon kwanaki.

Masu sharhi sun ce dukkan jihohin ukun na da matukar muhimmanci ga Trump idan har yana son wa’adi na biyu, kuma ya guji zama shugaban Amurka na uku a cikin shekaru arba’in da suka gabata da ya fadi neman sake tsayawa takara.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *