Tsohon sanata, Ifeanyi Araraume, ya zargi gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, da yi wa jam’iyyarsa ta APC makarkashiya a zabukan yankin Kudu.
Sanata Ifeanyi Araraume wanda yake ikirarin shi ne ‘dan takarar APC a zaben Imo ta Arewa da aka yi kwanan nan, ya bada shawarar a ja-kunnen gwamnan.
Punch ta ce tsohon ‘dan majalisar ya jefi Gwamna Hope Uzodinma da wannan zargi na zagon-kasa ne a tattauna da manema labarai a ranar Lahadi.
Inda yace gwamnan ya bawa ‘ya ‘yan APC umarni suyi wa PDP aiki a zaben cike gurbin da aka yi. Araraume yace tun farko dama ‘yan adawa ake ba mukamai a Imo.
Sanata Ifeanyi Araraume ya ke cewa gwamna Uzodinma ya yi duk yadda zai iya wajen ganin ya kawo masa matsala, amma a karshe jam’iyyar APC ta ci zabe.
Ararume ya caccaki gwamnan a game da ja da ya yi da hukuncin da babban kotun tarayya ta yi.
Gwamnan ya maida martani ta bakin wani hadiminsa, Modestus Nwamkpa, wanda yace karyar banza ce kurum Ararume yake yi, yace mai gidansa su ne APC.
A daidai wannan lokaci ne kuma mu ka ji cewa masu aikin share-share a jihar Imo sun tare kofar shiga gidan gwamnati a Owerri, domin nuna wa gwamna fushinsu.