Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An yi nasarar yi wa Sarkin Saudiyya Salman Bn Abdul’aziz tiyatar mafitsara a asibitin King Faisal da ke Riyadh, babban birnin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya sanar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ci gaba da cewa Sarki Salman zai shafe wasu kwanaki a asibitin don ci gaba da kula da lafiyarsa bisa shawarar tawagar lafiyar da ta duba shi.

A ranar Litinin 20 ga watan Yulin nan ne Saudiyyar ta sanar da batun kwantar da Sarki Salman a asibitin Riyadh inda ake yi masa gwaje gwaje.

Bbc ta ruwaito bayanai nacewa Sarkin mai shekara 84 na fama ne da rashin lafiyar da ta shafi mafitsara.

Tun 2015 Sarkin ke mulki a Saudiyya – kafin zamansa Sarki ya shafe shekara kusan biyu a matsayin Yarima mai jiran gado kuma ya taba rike mukamin mataimakin firimiya a 2012.

Ya kuma shafe sama da shekaru 50 a matsayin gwamnan Riyadh.

shugabannin kasashen duniya da dama ne suka dinga aike wa sarkin sakon fatan samun sauki da gaggawa, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu mai bai wa Biharin shawara kan yada labarai ya fitar, Shugaba Buhari ya yi masa addu’ar fatan samun sauki cikin gaggawa a madadinsa da kuma al’ummar Najeriya.

Ya kuma bayyana Sarki Salman a matsayin shugaba mafi nagarta da ya taɓa haɗuwa da shi a yayin mu’amularsa da sauran shugabannin duniya.

“Sarki Salman aminin Najeriya ne na haƙiƙa wanda bai taɓa kasawa ba ko nuna damuwa ta ko wane ɓangare kan dukkanin muhimman buƙatu da kyakkyawar alaƙa,” inji Buhari.

Labarin rashin lafiyar Sarki Salman Yanzu ya sa hankali ya karkata ga makomar Saudiyya musamman zamanin Muhammad Bin Salman, Yarima mai jiran gado wanda tuni ake ganin shi ke tafiyar da jagorancin Saudiyya.

Yariman mai jiran gado shi ya kaddamar da sabbin sauye sauye na tattalin arziki na kokarin karkatar da dogaro da kasar Saudiyya ke yi da arzikin feitr.

Wannan ya sa Yariman mai shekara 34 ya samu karbuwa da goyon baya musamman tsakanin matasan Saudiyya na kawo wasu sabbin abubuwan da ba a taba gani ba a kasar musamman ba mata ‘yanci.

Amma wasu na bayyana damuwa kan nuna karfi iko akan kafofin watsa labarai da kuma kama-karya da aka gani.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *