Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ranar komawa aiki ga ma’aikata a fadin jihar baki daya.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce ma’aikatan gwamnati a jihar da ke mataki na 14 za su koma bakin aikinsu daga ranar Litinin 20 ga watan Yuli da muke ciki.
Sanarwar ta ce wajibi ne ga dukkan ma’aikatan su zama masu bin dokar da mahukunta a bangaren kiwon lafiya suka shimfida.
Ta cikin sanarwar gwamnatin Kaduna ta ce masu mataki na 14 zuwa sama za su rika zuwa aiki ne a ranakun Litinin da Laraba da kuma Juma’a.