Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An kammala muhawarar farko cikin muhawarori uku tsakanin Donald Trump na jam’iyyar Republican da Joe Biden ‘yan takarar mukamin shugaban kasar Amurka na shekarar 2020.

Tun kafin a je ko’ina, ‘yan takarar biyu suka far wa juna, inda suka kaure da bakaken maganganu da zage-zagen juna.

Mr Biden ya bayyana Shugaba Trump a matsayin “shashasha” sannan ya ce masa “rufe bakinka”. Mr Trump ya bijiro da batun shan kwayoyin dan gidan Biden.

Bbc ta ruwaito cewa Ra’ayoyin jama’a sun nuna cewa Mr Biden ya yi nasara a muhawarar da kashi 48, yayin da Mr Trump ya samu kashi 41, sannan kashi 10 suka ce ‘yan takarar biyu sun yi kankankan.

Babban dan jarida Chris Wallace na tashar talabijin din Fox ne ya jagoranci muhawarar, kuma ya tambayi ‘yan takararar tambayoyi shida-shida cikin batutuwa shida, inda aka ba su minti 15 domin amsa tambayoyin da mayar da martani.

Mutane kalilan ne aka bari suka halarci zaman, ciki har da iyalan ‘yan takarar na kusa da su. Matar Mista Trump Melani da matar Joe Biden Jill sun harci muhawarar.

Ba a amincewa wadanda ke cikin dakin taron yin magana ko shewa ba domin nuna goyon bayansa ga wanda suke goyoin baya.

Saboda cutar korona an hana ‘yan takarar gaisawa da juna, kuma an tabbatar da tazara tsakaninsu.

Wannan ce muhawara ta farko cikin ukun da za su yi gabanin zaben shugaban Amurka ranar 3 ga watan Nuwamba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *