
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sassauta dokar kulle ta mako huɗu da ya saka a Jihar Kano da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da korona, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja a yau Litinin.
Sai dai Boss Mustapha, wanda shi ne kuma sakataren gwamantin tarayya, bai bayyana takamaimai abin da sassautawar ke nufi ba.
Ya bayyana cewa an shiga zango na biyu na sassauta dokar kulle a Najeriya, wanda zai yi mako huɗu nan gaba kafin a sake duba ta.