Gwamnatin jiha karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ta bada sanarwar dage dokar hana zirga zirga domin shirin azumin Ramadan. Da’ge dokar na rana daya ne wanda zai kasance gobe Alhamis 23 ga watan April daga karfe 6am na safe zuwa karfe 12 na daren gobe Alhamis. Ranar jumaah babu zirga zirga har zuwa tsahon mako daya inda daga bisani gwamnati zata sake dubawa domin sake daukar mataki.
Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
April 22, 2020.