Daga-Abubakar Sale Yakub

Shugaban Kungiyar Battlers dake yaki da shaye shaye da laifuffuka, Alhaji Salisu Ibrahim Zage, ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Wakilinmu Abubakar Sale Yakub, a yau din nan.
Da yake Magana akan yadda suke aiki tare da sauran hukumomi da kungiyoyi yace an samu raguwar shaye shaye, Salisu Zage,yace Kungiyar Battlers yanzu haka tana aiki da Ma’aikatar Mata ta jihar Kano, wadda ta basu guraben horar da sana’o’i biyar ga mata.
Salisu Ibrahim Zage, yace domin rage yawaitar shaye shaye akwai bukatar iyaye surika jan kunnen ‘ya yansu akan illar shaye shaye wanda hakan zai rage yawaitarsa a fadin Kasar nan