Ma’aikatar lafiya ta jihar Lagos ta bayyana cewar, an sami karin mutane uku wadanda ake zargin suna dauke da cutar Coronavirus a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Akin Abayomi ya bayyana hakan a jiya Alhamis, inda ya kara da cewar wadanda ake zargin tuni aka killace su a wani waje na musamman dake Yaba a jihar.
Ya kara da cewar wadanda ake zargin sun fito ne daga kasashen Faransa da Burtaniyya da kuma Sin, sannan kuma ana cigaba da gudanar da binkice domin ganin suna dauke da cutar ko kowa basa dauke da ita.
An fara samun bullar cutar a kasar nan,a satin daya gabata, bayan wani dan’kasar Italiya wanda yazo kasar nan, aka kuma gwada shi aka tabbatar yana dauke da kwayar cutar.
Tun lokacin bullar cutar, Gwamnatin tarayya take kokarin ganin cewar an dakile dukkanin hanyoyin yaduwar cutar.
