
An sallami Priministan Birtaniya daga asibiti bayan ya murmure daga cutar covid-19 wadda yayi fama da ita.
Boris Johnson, an kaishi cibiyar da ake kula da mutanen da jikinsu yayi tsanani run a ranar Alhamis an kuma dawo dashi sashin da ake kai wadan da cutar bata galabaitar dasu ba a yau Lahadi.
Ya ce zaicigaba da zama bisa shawarwarin da likitansa ya bashi dan kada ya sake nuna alamun cutar.
Har wa yau a wata sanarwa da Downing Street ta fitar a ranar lahadin nan tace Boris ba zai dawo bakin aiki yanzu ba.
A wata shawarar da tawagar likitoci suka bashi sun fadawa Priminstan cewa ba zai dawo aiki yanzu ba.
“Ya kuma godewa kowa da kowa a St.Thomas bisa kulawar daya samu”
kuma “yiwa wadan da suka kama da cutar fatan samun sauki daga covid-19.
Zuwa yanzu mutane sama da dubu 84 suka kamu da cutar a Burtaniya, yayin da a yau aka samu mutane sama da Dari 7 da suka rasa rayukansu.