Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An sallami Aishwarya Rai Bachchan da ‘yarta Aaradhya daga asibiti bayan an yi musu gwajin korona an tabbatar sun warke.

Jarumar fina-finan na Indiya, kuma wacce ta taba samun lambar yabo a sarauniyar kyau ta duniya, sun bar asibitin Nanavati ne tare da ‘yarta a safiyar ranar Litinin.

Mijinta Abhishek Bachchan, ya wallafa sakon godiya a shafinsa na tuwita inda yake gode wa ‘yan uwa da abokan arziki saboda addu’ar da aka yi musu shi da iyalansa da ma mahaifinsa a kan samun sauki daga cutar korona da suka kamu da ita.

Sai dai Abishekh da mahaifinsa Amitabh Bachchan har yanzu suna asibitin inda suke karbar magani.

Amitabh Bachchan: Shahararren ɗan Bollywood ya kamu da korona
Coronavirus a India: Indiyawa na yi wa Amitabh addu’ar samun sauki
A farkon watan da muke ciki ne aka kwantar da su a asibiti bayan an yi musu gwaji an ga suna dauke da cutar korona.

Aishwarya da ‘yarta sun godewa jama’a saboda addu’oin da aka yi musu, kuma tuni suka koma gida.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *