An sake dakatar da kakar wasan kwallon ƙafa a Peru , kwana ɗaya bayan an dawo wasan.
An ɗauki wannan matakin ne sakamakon yadda ‘yan kallo suka ƙi bin dokokin korona inda suka ƙi bayar da tazara a tsakani.
Dubban magoya bayan kulob ɗin Universitario suka yi fitar farin ɗango a ƙasar a ranar Juma’a kafin buga wasan su na farko tun bayan da aka dakatar da ƙwallon ƙafa a ƙasar watanni biyar da suka gabata.
Wannan ne ya sa gwamnatin ƙasar ta shiga lamarin sakamakon fiye da mutum dubu 20 da suka mutu a ƙasar sakamakon wannan cuta.
Ƙasar Peru ita ce ta uku a yawan masu korona a yankin Latin Amurka bayan Brazil da Mexico.