Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta tabbatar da sace masallata 18 da kashe mutum biyar yayin da ake gudanar da Sallar Juma’a a garin Dutsin Gari da ke Ƙaramar Hukumar Kanoma a jihar.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar SP Muhammed Shehu ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun saje da masallatan inda a lokacin da ake shirye-shiryen sallar suka gudanar da wannan aika-aikar.
A cewarsa, “bayan ‘yan bindigan sun tarwatsa masallatan, sai suka kwashi wasu suka yi daji da su, sannan a cikin harbin da suka yi, mutum biyu suka rasa rayukansu, amma kuma daga baya cikin waɗanda suka ji rauni mutum uku sun rasu, wanda hakan ya sa suka zama biyar”.
Wasu mazauna ƙauyen sun bayyana cewa masallata 40 ne aka sace, ciki har da limamin masallacin, amma dai rundunar ‘yan sanda reshen jihar ta kafe cewa mutum 18 ne aka sace, kuma ban da liman a cikinsu.