Wata gobara da ta riƙa ci har tsawon wata biyar a rijiyar man fetur da ke arewa maso gabashin Indiya, a ƙarshe dai an kashe ta a yau Lahadi.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ma’aikatan kamfanin Oil India sun yi ta yaƙi da wutar a Jihar Assam tun bayan da aka samu wata fashewa a watan Yuni, inda rijiyar man ta fashe kuma ta fara tsiyayar da ɗanyen gas.
Ma’aikata biyu ne suka mutu sakamakon fashewar. Daga baya wani mutum ɗaya ya sake mutuwa a watan Satumba bayan wata fashewar a wurin.
Ƙwararru daga ƙasashen Canada da Singapore da Amurka ne suka haɗa ƙarfi da ƙarfe domin kashe wutar.
Bbc ta ruwaito wani mai magana da yawun Oil India, Tridiv Hazarika, ya bayyana cewa “an kashe gobarar kwatakwata”.
“An kashe wutar kuma yanzu an kawo ƙarshenta,” in ji shi a hirarsa da AFP. “Babu sauran wuta a rijiyar yanzu kuma za a kula da ita na tsawon awa 24 domin ganin ko akwai sauran gas.”
An ɗebe dubban mazauna ƙauyuka a yankin Tinsukia zuwa sansanonin agaji bayan gobarar ta fara ci a watan Yunin 2020.