daga -Abubakar Sale Yakub

‘Yan sandan Saudiyya sun kama mutanen 20 wadan da suke dinka rigar Ka’aba ta jabu a cikin wani gini dan su sayar akan makudan kudade.
Wajen dinka rigar Ka’abar mallakin ‘yan Nahiyar Asia ne wadan da aka gano sabuwar hanyar da suke cutar jama’a a kasar Saudiya; mutanen dai sun zone daga kasashen.
A cewar rahitonnin da wata kafar yada labarai ta Saudiya ta fitar, tace mutanen suna dinka Kiswa wato rigar Ka’aba dan su damfari mutane kudade masu yawa da cewar Rigar Ka’abace ( Kiswa).
Wannan dai labari ya girgiza al’ummar Musulmi ganin cewar Kiswa da shi ake rufe Dakin Allah.