Daga -Zaharadden Abdullahi Bichi,

Hukumar Kula da Ingancin abinci da kayyakin da kamfanoni suke sarrafawa reshen Jihar Kano, tace ta samu nasarar kama magunguna da Lemuka da Shinkafa da Fulawa da wadan da wa’adinsu ya kare akalla Trailer biyar.
Shugaban Hukumar Farfesa Yusuf Ibrahim Sabo, ya bayyana hakan kwanaki kadan bayan Hukumar ta kama wata Fulawa aikin hadin guiwa da Jami’an KAROTA.