
Mahukuntan Saudiyya sun dakatar da yin sallah a dukkan masallatan kasar, idan ban da masallacin Ka’abah da kuma na Madina, a cewar kamfanin dillacin labaran kasar.
A baya dai mahukuntan Saudiyya sun hana masu zuwa aikin Umrah da na Hajji siga kasar saboda yaduwar cutar coronavirus.
An dauki matakin ne makonni kadan kafin azumin watan Ramalana inda Musulmi kan yi tururuwa zuwa kasar domin gudanar da ayyukan ibada.
Ya zuwa yanzu, mutum 133 aka tabbatar sun kamu da cutar a Saudiyya.