Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga Abdullahi Isa

Yayin da kwayar cutar corona ke cigaba da fantsama a kasar nan, kwararru a harkar kiwon lafiya sunja hankalin mahukunta dasu daina kawar da kai daga sauran cututtuka masu hadari ga rayuwar alumma.

Wani kwararren a ilimin fannin kiwon lafiya , Dr. Abubakar Ibrahim Hassan, shi yayi jan hankalin lokacin da yake zantawa da Editan Labaran Express radiyo Abdullahi Isa.

Masu lura da al’amuran yau da kullum , sunce galibi, Gwamnatoci , kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki sun kawar da kansu daga ssursn cututtuka masu illa ga Dan Adam, inda suke mayar da hankali kacokan kan matakan kariya da yaki da cutar coronavirus.

Hakan kuma na nufin marassa lafiya dake fama da cututtaka daban-daban,basa samun kulawar data kamata tun bayan da cutar corona ta shigo Najeriya.

Amma Dr. Abubakar Hassan yace” wajibi ne mahukunta su farga kan wannan mas’alar.

Dr. Abubakar Hassan wanda malami ne a sashen koyar da lafiyar Dan Adam da motsa jiki a jami’ar Bayero ta Kano, ya roki gwamnatin jahar Kano kan ta samar da wadatattun kayan kariya ga likitoci domin su sami sukunin kula da marasa lafiya ba tare da fargabar kamuwa da cututtuka masu yaduwa ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *