Kasashen duniya, musamman a nahiyar Turai, sun yi matukar mamakin yadda annobar korona bata hallaka mutane da yawa a nahiyar Afrika ba
Tsohon kakakin tsohon shugaban kasa Jonathan, Doyin Okupe, ya ce yana da kwafin wani rahoto da likitoci fiye da 100 suka sanyawa hannu
A cikin rahoton, Okupe ya ce an alakanta karfin garkuwar jikin mutane da adadin sinadarin Vitamin D3 da ake samu daga hasken rana
Cif Doyin Okupe, kakakin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya wallafa wata makala akan rashin tasirin kwayar cutar korona a tsakanin talakawa mazauna nahiyar Afrika.
Okupe ya yi ikirarin cewa yana da kwafin rahoton wani bincike Wanda masana kimiyya suka gudanar.
A cikin rahoton, Okupe ya bayyana cewa masana kimiyya sun alakanta karfin garkuwar jikin mutane da sinadarin vitamin D3 wanda ake samu daga hasken rana, na daga cikin wasu dalilan
Ya ƙara da cewa samun sinadarin Vitamin D3 na bada garkuwa da kuma rigakafin annobar COVID-19 kuma yawanci talakawa sun fi masu hali yawan wannan sinadarin