Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rashin jituwa ta kaure tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyoyin masu bukata ta musamman saboda fara kamen mabarata.

Cikin mutanen da aka kama sun hadar da makafi, da guragu, da kurame mata da tsofaffi.

Wasu daga cikinsu sun shaida wa BBC cewa jami’an tsaro sun cafke su ne ranar Juma’a, a babban birnin jihar, lokacin da suke bara a kan tituna.

”An kama mutane da yawa, wasu a Kawo, wasu a Unguwar Sarki, wasu a Kano Road” In ji wani mabaraci da muka zanta da shi.

Wasu daga cikinsu sun yi korafi a kan munin yanayin wurin da aka ajiye su, ga shi babu abinci babu ruwan sha kamar yadda mutumin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana.

”Wani wuri ne ma, akwai kashin awaki, nan muke fitsari, ga sauro, ba abinci, kuma tun da aka kama mu babu wanda ya kawo mana abinci, sai dai wadanda suke da kudi in masu abinci sun kawo su saya”

To sai dai gwamnatin jihar a ta bakin Hafsat Muhammad Baba, kwamishiniyar kula da walwalar jama’a ta ce daukar wannan mataki ya zama dole ganin yadda mabaratan ke saba dokokin da aka gindaya, da kuma rashin bin ka’idojin gwamnati.

 

Ta kuma ce wasu al’umomin da ke zaune a wuraren da suke bara ne suka gabatar da ƙorafi a kan yadda almajiran suke ɓata muhalli.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *