Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga -Abubakar Sale Yakub

Hukumar jin da din alhazai ta Jihar kano tace” a bana bujiro da wani sabon tsari na haska Majigi dan ganin yadda ake aikin hajji a lokacin bita ta Mako-mako wanda hakan zai saukakawa Maniyata saurin fahimtar aikin a bayyane”.

Babban Sakataren Hukumar Muhammad Abba Danbatta, ya firta hakan a lokacin da yake jawabi a wajen bude bitar Alhazan Jihar Kano a makarantar koyon harshen Larabci ta S.A.S.

Abba Danbatta, yace za’a saka majigin a cibiyoyin 32 dake jihar Kano, yana mai cewa za’a iya sakawa kowanne Maniyaci Hoton Vedio ko muryar bayanan aiki hajji.

Babban Sakatren ya kuma ja hankalin Maniyata dasu mayar da hankali wajen halartar bita wanda ta hakane zasu san yadda zasu gabatar da ibadar aikin hajji.

Da yake jawabi tun dafari shugaban Hukumar jin da din alhazan ta Juhar Kano, Farfesa Abdullahi Sale Pakistan, ya bayyana aikin hajji a matsayin ibadah wanda kuma ya zama majibi a nemi ilimin sa dan samun dacewa.
Ya kuma sake yin kira ga Maniyata dasu surika halartar bita ako da yau she.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *