Runduna ta musamman ta sojin Najeriya, ta yi nasarar cafke shugaban matsafar kungiyar asiri ta Gana, Mr. Ugba Iorlumun, wanda ake zargi da kashe tare da amfani da sassan jikin mutum don tsafi.
Kwamandan runduna ta musamman ta 4, Maj.-Gen. Gadzama, ne ya bayyana haka ranar Laraba a garin Lafiya yayin da ya ke holin yan kungiyar asirin Gana su 41 tare da masu garkuwa 25 da kuma yan fashi da makami.
A ta bakin Kwamandan ya ce “Ina mai matuƙar farin ciki sanar da ku cewa, yan kungiyar asirin Gana su 41 suna hannunmu. Adadin da ya kai su 119 da muka baza komar nemansu.
“Kafin wannan lokaci, babban laifi ne ka ambaci sunan Gana cikin ƙabilar Tiv, Jukun ko ta Kuteb saboda tsoron mutanen sa na iya kamo mutum su kai masa ya dafa.”