Ko a baya an samu taƙddama tsakanin Najeriya da Ghana bayan rufe shagunan ‘yan Najeriyar a birnin Accra kafin ƙura ta lafa
Shugaban Ghana ya bai wa gwamnatin Najeriya tabbacin kama mutanen da ake zargi da rusa wani ginin ofishin jakadancin Najeriya a birnin Accra a ƙarshen makon jiya.
Bbc ta ruwaito Shugaba Nana Akufo Addo, yayin zantawa da takwaransa Muhammadu Buhari ta wayar tarho ranar Talata, ya amsa cewa an yi kuskure wajen rusa ginin da ke cikin ofishin jakadancin Najeriya a ƙasarsa.
Babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa shugaban na Ghana ya kuma nemi afuwar Najeriya kan wannan abu.
Rusa ginin da wasu mutane suka yi ranar Asabar a Accra, babban birnin Ghana, ya janyo ɓacin rai da kuma sake tayar da batun rashin jituwar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Al’amarin dai ya janyo kiraye-kiraye a Najeriya cewa gwamnati ta ɗauki matakin ramuwar gayya kan wannan abu da suka bayyana da “cin fuska ga Najeriya”.
Malam Garba Shehu ya ce daga bayanan da suka samu “wani basarake ne a birnin Accra da ke ji da isa da kuma ƙarfin mulki ya ɗauki katafila ya je ya rushe wannan gini”.
Sai dai ya ce amma bincike ne kawai zai tabbatar da duk abin da ya faru da kuma duk waɗanda ke da hannu cikin wannan al’amari da kuma dalilansu na yin wannan aika-aika.
Ko da yake, mai magana da yawun shugaban Najeriyar bai ce ga ranar da za a kammala binciken ko kuma gurfanar da mutanen da aka kama gaban kotu ba.
Da aka tambaye shi game da iƙirarin da wasu rahotanni ke yi cewa mutanen da suka rusa ginin na yi cewa Najeriya ce ta je take gini a wani filin da ba bisa ƙa’ida ba. Garba Shehu ya ce wannan zance bai ma taso ba.
Ya ce a tsarin diflomasiyya, ba yadda za a yi ofishin jakadancin wata ƙasa ya je ya yanki fili kawai a wata ƙasa ya kama gini. “Dole sai an ba da izini,” in ji shi.
A cewarsa kuma yayin da aka ba da izini, aka damƙa shi a hannun wata ƙasar waje, to kariyar diflomasiyya ta hau kan wannan wuri.
Ya ce babu ma wata doka da za ta iya yin aiki a cikin wannan farfajiya ta wannan ofis, face dokar Najeriya. “Dokar Ghana ba za ta iya shiga ta yi aiki a wurin ba, sai dai dokar Najeriya”.
Garba Shehu ya ce duk sun ji kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya suka yi ta yi bayan aukuwar lamarin musamman ma jam’iyyar adawa ta PDP.
A cewarsa: “To, so suke Najeriya ta fito ta yi yaƙi da Ghana? Abin ya zama rashin hankali ke nan”.
Ya ce magana ce ta akwai matsala. Kuma yaya za a yi a gyara wannan lamari. A bar shugabannin nan su yi abin da yake daidai, ba tare da tashin hankali ko kawo fitina a tsakanin al’ummomin ƙasashen nan ‘yan’uwan juna ba.