A karon farko bayan sama da shekaru Talatin ana shirya gasar Dala hard Court a jihar kano hukumar dake shirya gasar ta fitar da sanarwar dage gasar bana 2020 zuwa shekara Mai zuwa ta 2021,
A wata takarda mai dauke da sa hannun daraktan gasar Malam Yusif Datti ta bayana dage gasar a matsayin wani abu daya zama dole saboda halin kula da lafiya musamman abinda ya shafi harkar wasanni a duniya baki daya,
Cutar Corona virus ta tsaida alamuran duniya cik a baya ciki harda harkokin wasanni Wanda har iyanzu abubuwan basu koma dai dai ba.
Hukumar ta kara da cewa 2021 zata zama sabuwar shekarar tarihi bayan tsallake shekara guda a karon farko bayan 33 ana gasar ba tare da tsayawa ba.