Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Daga Jegus

Sakamakon bullar cutar coronavirus a kasashen duniya, an daga wasannin Serie A biyar da za a buga a karshen wannan makon ciki kuwa har da karawa tsakanin Juventus da Inter Milan.

Haka zalika wasan da za a yi tsakanin Udinese da Fiorentina da karawa tsakanin AC Milan da Genoa duka na cikin wadanda dagawar ta shafa.

A baya dai an yi niyyar buga duka wasannin ba tare da ‘yan kallo ba, sai dai daga baya Serie A ta dauki matakin daga wasannin a safiyar Asabar.

A halin yanzu an saka ranar Laraba 13 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a buga wasannin.

Sakamakon bullar cutar, wasan karshe na gasar Coppa Italia wanda aka yi niyar bugawa a ranar, an matsar da shi gaba zuwa Laraba 20 ga watan Mayu.

Wasannin da za a buga a Lazio da Napoli da lecce da kuma Cagliari na nan daram kuma magoya baya za su je kallo, sai dai har yanzu babu tabbaci dangane da ko za a daga wasan da Sampdoria za ta yi a ranar Litinin

A ‘yan kwanankin nan dai hukumar FIFPRO ta fitar da wata sanarwa inda ta ce a akwai barazanar harkokin kwallon kafa na iya zama “hanyar yada” cutar.

Hukumar ta bayyana cewa ‘yan kwallon sun fara damuwa game da yaduwar Coronavirus inda suka fara tuntubar hukumomi saboda tsoron ana iya tilasta musu yin wasa a ”wurare masu hadari sosa.”.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *