A Jamhuriyyar Nijer dake yammacin afrikakotun tsarin mulkin kasar ta bayyana sunayen mutanen da suka cancanci shiga zaben shugaban kasa na ranar 27 ga watan Disamba da ke tafe bayan gudanar da aikin tantancewa amma kuma ta yi watsi da wasu daga cikin ‘yan takarar.
A zamanta na yammacin jiya Juma’a a karkashin shugabancin mai shari’a Bouba Mahaman, kotun tsarin mulkin kasar ta sanar da sunayen mutanen da suka cancanci shiga zaben ranar 27 ga watan Disamba. Daga cikin ‘yan takara 41 da suka shiga fafatawar. Kotun ta ce ‘yan takara 30 ne suka cika sharuddan da ya kamata.
Dan takarar jam’iyyar PNDS Bazoum Mohamed na daga cikin wadanda suka sami izinin shiga zaben, ya yi godiya ga Allah ya kuma ce zai tabbatar da ya ci gaba da aiki tare da jam’iyyar sa.
Kotun ta yi watsi da takardun ‘yan takara 11 saboda rashin cika ka’ida, akasarinsu wadanda suka gaza biyan kudaden jingar da aka kayyade ne, sai kuma jagoran ‘yan adawa Hama Amadou na jam’iyyar Moden Lumana wanda hukuncin da aka yanke masa a shari’ar nan ta badakalar jarirai ta goga wa takardunsa bakin fenti.