Bayan kimanin shakaru 6 batare da anyi gasar wasan kwallon kafa tsakanin kananan hukumomin jihar kano da aka sabayi duk shekara ba,
A ranar lahadi 1ga watan Oktoba ne aka sanya harsahin gasar a wani tsari na fara wasan dan motsa gasar kafin farata gadan gadan inda aka fara wasan da kungiyayi 8 a filin wasa na Dr Abdullahi Umar Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Kudu,
An dauki tsawon lokaci ana kokarin dawo da gasar amma hakan bayyiwu ba sai wannan lokacin da gasar ta samu sahalewar Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Goyon Bayan Kwamishinan Kananan Hukumomi Honourable Murtala Sule Garo,
A jawabinsa yayin bude gasar a madadin Gwamnan jihar kano kwamishinan matasa da wasanni kwamared Kabiru Ado Lakway cewa yayi wasannin kananan hukumomi wani abune da yake bunkasa cigaban matasa da hada kawunansu a fannoni daban daban na rayuwa tare da zakulo matasa masu basira dan daga darajarsu a fagen wasanni,
Shi kuwa wakilin karamar hukumar Dawakin kudu a majalisar wakilai ta kasa Hon Mustafa Bala Dawaki Maigidan Ruwa Wanda kuma ya Samar da filin wasan garin dawakin kudu, bayyana ranar yayi da cewa ranace abar alfahari a gareshi da alummar Dawakin kudu, inda yace taron. daya Gani ya karfafa masa gwiywa tare da shan alwashin daga darajar filin wasan Idan bukatar hakan ta taso,
Wasannin da aka gabatar sun hadarda na Kabo 1-3 Garun Malam., Dawakin Kudu 2-1 Gabasawa, fagge 2-1 Bagwai yayin da Gwale da Bebeji suka 0-2 inda Bebeji tayi nasara a wasan yamma wasan da yaka alamta bude gasar ta Bana dukkannin wasannin za sada zumuntane.