Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An bawa kamfanin TCN waadin kammala aikin walalanbe,Shugaban kwamitin wutar lantarki na majalisar wakilai ta kasa Injiniya Magaji Da’u Aliyu ya baiwa kamfanin samar da wutar lantarki ta kasa TCN waadin 1st December 2020 da su kammala aikin karamar tashar samar da wutar lantarki ta walalambe dake yankin karamar hukumar Nasarawa a jihar kano ko su fuskanci fushin majalisar wakilai,

Injiniya Da’u wanda cikin rashin jin dadi ya nuna rashin gamsuwa da yadda aikin ke gudana ya umarci kamfanin dasu gabatar da tsarin abin da suke bukata kai tsaye zuwa ofis dinsa cikin gaggawa dan daukar matakin daya dace,

Shugaban kwamitin wutar ya kara da cewa kakakin majalisar wakilai ta kasa Femi Bajabiamila ya damu kwarai da yadda aikin ke tafiyar Hawainiya, ya bada tabbacin ganin aikin ya samu kammaluwa cikin wadannan waadin daya bayar,

Da yake jawabi dan majalisar wakilai mai wakiltar Nasarawa a birnin kano Nasiru Ali Ahmed ya godewa shugaban kwamitin duba da yadda ya karbi kukan a kankanin lokaci duk da irin yadda ayyuka suka shamasa kai, shima dayake Karin haske kan yadda aiki ke tafiya dan majalisa mai wakiltar Wudil da Garko Injiniya Mohammad Ali Wudil yace sama da shekaru goma ake ta kokarin wannan aiki amma abin takaici hakan bai cimma ruwa ba in banda yanzu da shugaban kwamitin Da”u Aliyu ke kokarin tabbatar dashi.

A jawabansu daban daban wakilan TCN da KEDCO sun yabawa shugabancin majalisar da shugaban kwamitin bisa yadda suka nuna damuwa kan ayyukan inda sukayi alkawarin bada cikakken goyon baya da ganin an samu nasara,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *