Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A yau Lahadi 13 ga watan Disambar 2020 ne aka daura auren matashi dan jihar kano Isa Suleiman Panshekara da sahibarsa ‘yar Amurka, Janine Sanchez.

Tsohon sanata mai wakiltan mazabar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ne waliyin amarya Janine Sanchez kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Al’umma da dama sunyi tururuwa zuwa masallacin Juma’a na Gasau da ke karamar hukumar Kumbotso don shaida daurin auren da ake dade ana fatan ganin ranar bayan da masoyan biyun sun dauki lokaci suna soyaya.

Angon ya biya sadaki na Naira Dubu 50 lakadan ba ajalan ba.

Mahaifin ango Malam Suleiman a zantawar da ya yi da BBC ya ce an daura auren ne bayan an amince da dukkanin sharuddan da ya gindaya.

Cikin manyan bakin da suka halarci daurin auren sun hada da Sanata Shehu Sani da kuma shugaban karamar hukumar Kumbotso na Jihar Kano.

Jenine Sanchez ta fara soyayya da Suleiman Panshekara ne ta dandalin sada zumunta na Instagram bayan ya burge ta da gaskiyarsa ta hanyar ankarar da ita game da wasu ‘yan damfarar intanet.

Anngo Isa ya ce iyayensa sun amince masa da auren masoyiyarsa Jenine kuma nan da watan Maris za a yi bikinsu daga bisani kuma su lula Amurka tare.

“Bayan bikin mu a watan Maris insha Allah, za mu wuce Amurka inda nake sa ran samun aiki ko na koma makaranta sannan in samu kungiyar da zan dinga buga wa kwallo”, in ji shi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *