Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An bayyana samun masu cutar korona 453 a Najeriya ranar Asabar, abin da ya sa adadin mutanen da annobar ta shafa zuwa yanzu ya kai 46,140.

Alƙaluman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ke fitarwa kullum, sun nuna cewa cutar ta kuma yi sanadin mutuwar shida cikin sa’a 24.

Abuja ce a wannan karo ta fi yawan masu fama da cutar da mutum 75, yawan masu korona a Abuja zuwa yanzu ya haura 4,300.

Ƙididdigar ta kuma nuna cewa mutum 407 ne suka warke daga cutar kuma har an sallame su daga cibiyoyin kwantar da masu korona na ƙasar.

Bayanan NCDC dai na cewa marasa lafiyan da ke ci gaba da jinyar cutar korona yanzu mutum 12,114 ne a faɗin ƙasar, bayan warkewar dubban mutanen da aka samu ranar Talata.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *