Alkaluman wadanda suka kamu da cutar corona a najeriya sun haura dubu goma sha biyar kamar yadda hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasa suka nuna bayan samun sabbin wadanda suka kamu da cutar 627.
Adadin da aka samu ya nuna Har yanzu jihar legas ce kan gaba da yawan wadanda suka kamu da cutar a ranar juma a da mutum 229 da suka kamu a sa a 24.sai babban birnin tarayya Abuja mutum 65 sai Abia 54 da suka kamu sai Jihar Borno 42 sai Oyo da mutane 35 Rivers 28, Edo 28 sai Gombe 27 da Ogun 21 plateau18 sai Delta da mutane 18, jihar Bauchi da Katsina nada mutum 10 kowannensu sai Benue 9 sai Ondo 8 kwara 6 Nasarawa da Enugu hurhudu kowannensu sai Sokoto,kebbi da Neja 3 kowannensu sai Kano da Yobe nada 1 kowanne.
Kawo iyanzu hukumar NCDC tace adadin wadanda suka warke sun doshi dubu biyar.