Alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria suna saka damuwa a zukatan jama’a tare da fargabar cewa za’a koma gidan jiya.
Mutane 930 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Laraba, 16 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.
Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 75,062 a Najeriya.
Daga cikin mutane sama da 70,000 da suka kamu, an sallami 66,775 yayinda 1190 suka rigamu gidan gaskiya.
Ga jerin adadin wadanda suka kamu a jihohin Najeriya:
Lagos-279
FCT-179
Plateau-62
Kaduna-54
Kano-52
Katsina-52
Imo-42
Jigawa-42
Rivers-38
Kwara-30
Nasarawa-19
Yobe-15
Ogun-13
Borno-10
Oyo-9
Niger-9
Ebonyi-6
Bauchi-6
Edo-5
Taraba-4
Sokoto-2
Cross River-2