Shugaban kungiyar kwallon kafa ta kano pillars Surajo Yahaya Jambul, yace alkalancin wasan firimiyar bana wata yar manuniyace da take haska irin jajircewa da akayi dan daga darajar wasan kwallon kafar najeriya a idon duniya,
A wata tattaunawa da yayi da Express Radio ya bayyana yadda a bana alkalan wasan ke jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da cewa abin ayabane,
Surajo jambul ya Kara da cewa mutukar yadda akai alkalanci a zangon farko ya dore, to akwai kyakykyawan zaton samun gagarumar nasara da zata zama abin alfahari ga kowa afadin kasarnan.