
Majalisar Dinkin Duniya tace Gidauniyar hamshakin attajirin Najeriya Aliko Dangote ta zuba kudin da ya kai naira biliyan guda da rabi cikin asusun yaki da annobar coronavirus wadda ke cigaba da lakume rayukan jama’a a fadin duniya.
Majalisar tace wannan hadin kai tsakanin Gidauniyar Dangote da Majalisar zai taimakawa gwamnatin Najeriya sosai wajen karfafa bangaren kula da lafiya da kuma taimakawa wadanda suka kamu da cutar wajen samun kular da ta dace.
Majalisar tace za’ayi amfani da wadannan kudade wajen sayan kayayyakin kula da lafiya da aka fi bukata da suka shafi kayan gwaji da na’urorin aiki domin yaki da cutar COVID-19.
Shugaban Gidauniyar Aliko Dangote yace illar da cutar COVID-19 ta shafi kowa kuma babu wani bangare da zai shawo kan ta shi kadai, abinda ya sa ya zama wajibi ga kungiyoyi masu zaman kan su su bada gudumawa domin yaki da wannan abokiyar gaba.
Dangote yace bukatar su itace marawa gwamnati baya yaki da cutar da kuma tabbatar da ganin an dakile ta.