Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wani makusancin marigayi Ali Kwara fitaccen Wanda yayi yaki da yan fashi da masu satar shanu Nazir Babaji Aliyu yace karya ce wasu mutane ikirarin nacewa marigayi Ali Kwara ya basu llakani,

A tattaunawar su da bbc hausa makusacin marigayin cewa yayi batun bada lakani ai shurkace kuma Ali baya shirka balle shi ya bawa wasu,

Ya kara da cewa ko abaya idan Alin zai fita kama yan fashi ko barayi baya tafiya da kowa acikin su, yace anma ko a baya mutane sun shayin sojan gona suce su Ali kwara ne

Nazir ya kara dacewa duk wanda a yanzu yake batun kusaci da Marigayi Ali a bayansa yake duba da cewa shine wanda yayi jinyarsa harya rasu kuma babu wsau mutane da suke zuwa wajensa kuma hankalinsa garau ya rasu balle ace wani Abu.

Kawo iyanzu tun baainisa da mutuwarsa ba har an fara samum wasu na zagawa cikin alumma suna cewa ya basu lakani,

A tattaunawarsu da BBC Hausa Nazir yace jama’a suyi hattara da masu yaudarar su suna karbe musu kudi

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *