Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.
Mutumin daya amfana da kayan abinci

Matar shugaban Kasa Dr. Aisha Buhari ta raba kayan abinci da Magunguna da kayan kariya daga cutar covid-19 ga al’ummar Jihar Kano ta karkashin gidauniyarta ta Future Assured.

Aisha Buhari tace an raba kayanne domin ragewa alummar jihar Kano halin da suke ciki , tana wannan jawabine a lokacin da take kaddamar da rabon kayan abincin ga marassa karfi dake Jihar kano, wadda ta samu wakilcin mai taimakamata Hadi Uba.

Yace sun fara rabon magunguna ga Asibitoci guda hudu da suka hadar da Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da Asibitin Shiek Jiddah wato (Coroda) da Asibitin Zana (IDH) da Kuma Asibitin Gidauniyar Future assured.

Hadi Uba, ya cigaba da cewa “wadannan magunguna za’a baiwa marassa lafiya kyauta, da kuma kayan kariya daga cutar corona, yayin da a ranar Asabar aka kaddamar da rabon kayan abinci a jihar Kano.

Har wa yau sun mikawa gwamnatin Jihar Kano wasu kayan domin rabawa alumma mabukata.

Da yake jawabi Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano Dr. Sheik Harun Muhammad Sani Ibn Sina, ya ce “hukumar Hisbah a shirya take ta bayar da gudinmawa wajen rabon kayayyakin ga mabukata dake kasa.

Wasu da mutane maza da mata suka amfana da Tallafin shinkafa da Taliya da man girki da sabulan wanka da wanki, a wasu daga cikin kananan hukumomin da suka hadar da Garko da Kura sun bayyana jin da din su tare da cewa kayan sun zo adaidai lokacin da ake bukatarsu.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *