Daga-Tijjani Ahmad Banyo

Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano ta dukufa wajen ganin an Gina cibiyar ko ta kwana ta killace mutanen da suka kamuda cutar coronavirus.
Kwamishinan Lafiya Na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya kai ziyarar ganin yadda aikin yake tafiya a Fililn wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata, wanda gidauniyar Dangote foundation tare da hadin Gwiwar Gwamnatin jihar kano suka Samar.
Za’a gina Cibiyar wacce aka samar domin killace masu cutar covid-19 mai dauke da gado 500 kuma tana da fangaruriebiyu wnada aka ware na maza dana mata.
Wlikimu Tijjani Ahmad Banyo, ya ziyarci filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata, inda yaganewa idonsa yadda aikin gina cibiyar ta covid-19 yake wakana
Ya kuma shaida mana cewa aikin wand aka fara shi a jiya Alhamis yana tafiya cikin sauri gamida kulawar kwamishin lfy na jihar.
Ya aiko mana dace kwamishinan lafiya yana jan hankalin alummar kano dasu mai da hankalinsu wajen kulawa da tsaftar jiki data mahalli.
Ya kuma ce ‘kamfanin Mai na Kasa NNPC ya shirya gina wata cibiyar a kano mai dauke da gadaje 200 wanda za kula da masu cutar coronovirus.