Kasashen afrika sun matsa kaimi ga hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya kan kaddamar dabinciken yadda ake nuna wariyar launin fata da cin zarafin bakake da yan sanda keyi a kasar Amurka.
Batun na daga cikin abinda taron hukumar zai tattauna akai a yau a Geneva,sakamakon kisan gilla da aka yiwa Geoge Floyd da kuma abin da ya biyo baya. ana yawan samun kashe kashen bakaken fata a kasar Amurka duk da ikirarinta na baiwa kowa damar watayawa a kasarta kamar yadda take ikirari,