Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a ranar Asabar, ya bukaci gwanatin tarayya da ta sanya dokar ta baci saboda matsalar tsaro a kasar nan bayan da yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai masu yawa a Katsina.

A wata sanarwa Atiku ya bayyana cewa dole gwamnati ta fito da sababbin dabaru ta kuma kyale tsofaffi.

“Sace dalibai masu yawa a makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a Jihar Katsina, abu ne wanda zai kawo cikas a yakin da ake da rashin tsaro a kasar nan, kuma ina Allah wadai,” a cewar Atiku.

Ina jajantawa iyayen yaran da abin ya afkawa da kuma gwamnati da al’ummar jihar Katsina, jihata kuma jihar marigayi mai gidana, Tafida Shehu Musa Yar’adua. Ina addu’ar Allah ya dawo da su cikin koshin lafiya.

“Ina mai kira ga jami’an tsaro da su dauki matakin gaggauta ceto yaran da aka sace, kuma bai kamata mu nade hannun mu zubawa matsalar rashin tsaro na ci gaba da ta’azzara a kasar nan. Dole ayi wani abu.

“Saboda haka ina kira ga gwamnati da sanya dokar ta baci da gaggawa a jihohin da yan tawaye da yan bindiga suka addaba, don shirin yakar su ko ta wani hali.

“Don kauracewa kokwanto, dokar da nake magana akai zata tafi bisa tsarin kundin mulkin kasa na 1999, ta hanyar saka dokar ta zata kula da gine ginen gwamnati ba tare da samun matsala ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *