Daga- Abubakar Sale Yakub

Ministan alamuran addinai na Saudiyya Sahibzada Noor-ul-Haq Qadri, ya ce a ranar Litinin ne 15 ga watan Yuni gwamnatin ƙasar za ta yanke shawara ta ƙarshe game da makomar Hajjin 2020.
Da yake bayani a wani taron tuntuba a ranar Alhamis, ministan ya ce gwamnatin Saudiyya za ta ɗauki matakin da ya fi dacewa saboda maniyyata aikin Hajji, sannan gwamnatin ta daɗe tana nazari tare da duba hanyoyi da dama game da aikin Hajjin.
Ya ce ana ci gaba da maharawa game da yadda za a tafiyar da aikin Hajjin a ma’aikatarsa, yana mai cewa Hajjin ba za ta kasance kamar yadda aka saba ba domin za a rungumi matakai na kaucewa yaɗuwar cutar korona.
Ma’aikatar lamurran addinin ta Saudiyya ta kuma ce ta bayar da umurni bincike kan ƙiyasin kuɗaɗen aikin hajji, idan har Saudiyya ta yanke shawarar taƙaita yawan maniyyatan da za su yi aikin Ibadaar da kuma adadin kwanakin da mahajjaci zai yi.