Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shubaban Amurka Donald Trump ya saka takunkumi a karon farko tun barkewar annobar korona.

An ga shugaban sanye da takunkumi ne lokacin da ya ziyarci wata asibitin soja da Washington inda ya gana da sojojin da suka ji rauni da kuma ma’aikatan lafiya

“Ban taba adawa da saka takunkumi ba amma nasan akwai lokaci da kuma wurin da ya dace,” a cewar Trump bayan ya fice zuwa Fadar White House.

A baya shugaban ya taba cewa ba zai taba sanya takunkumi inda ya yi shagube ga abokin hamayyarsa Joe Biden saboda ya sa takunkumi.

Amma a ranar Asabar ya ce “Ina ganin idan kana asibiti, musamman a wani yanayi, inda zaka yi magana a gaban sojoji da mutane da dama, ina ganin ya fi dacewa ka saka takunkumi.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *