Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i, ya sanar da cewa ya sake killace kansa bayan wasu na hannun damarsa da hadimansa sun kamu da kwayar cutar korona, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na tuwita.
El-Rufa’i ya sanar da hakan ne a wani sakon faifan bidiyo da ya wallafa a daren ranar Juma’a.
A cewarsa, ya killace kansa ne biyo bayan samun rahoton cewa wasu na hannun damarsa da makusanta iyalinsa sun kamu da kwayar cutar korona, kuma sun yi cudanya kafin fitowar sakamakon gwajinsu.
A ranar Alhamis ne El-Rufa’i yayi barazanar sake saka dokar kulle saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da ake samu a jihar da fadin kasa.
Abdallah Yunus Abdallah, mai taimakawa El-Rufa’i a bangaren watsa labarai, ya ce gwamnati za ta dauki wannan mataki ne saboda kare hakkin kare rayukan mutanen jihar ya rataya ne a wuyan gwamnan.