
Mabiya addinin Kisrista dake Sassan duniya sun gudanar da bikin Easter a gidajensu sakamakon yadda aka rufe mujami’u Sabo da tsoron yada cutar covid-19, hakan yasa Fafaroma Francis gabatar da jawabi kai tsaye ta kafafen internet.
A wannan mako da yake mai tsarki ga mabiya addinin Kirista, sun gabatar da ibadunsu ne, a cikin gidaje dan gudun yada cutar wadda ta harbi al’ummar duniya ku san miliyan 1.8
Bikin Easter yana da muhimmanci ga Kisristoci domin a irin wannan rana ce da Annabi Isa (A.S )ya koma ga mahaliccinsa Allah (S.W.A)